Tuesday, May 19
Shadow

Da Duminsa: Rahotanni sun bayyana cewa, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai zai fito takarar shugaban kasa a 2027, yayi martani

Wani na kusa da Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, El-Rufai zai tsaya takarar shugaban kasa.

Rahotan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.

Saidai a martaninsa ta bakin me magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, wannan Rahotan ba gaskiya bane.

Yace wani ne na kusa dashi ya bayyana ra’ayinsa amma ba daga bakinsa maganar ta fito ba.

Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ce ba zai ji tsoron fitowa ya bayyana ra’ayinsa na siyasa ba idan yanaso.

Karanta Wannan  Babban Fasto a Najeriya, Enoch Adebayo ya yi karin haske kan maganar cewa ya musulunta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *