Nafiu Bala Gombe ya fitar da jawabi a karin farko tun bayan da su Atiku suka yi babban zabensu na jam’iyyar ADC suka zabi shuwagabannin jam’iyyar.
Nafiu yace Zaben nasu ba halastacce bane kuma su ba halastattun ‘yan jam’iyyar ADC bane dan haka zaben da suka yi baya bisa doka.
Saidai kamar ko da yaushe yanayin yanda yake karatun nasa ya dauki hankula inda da yawa suka ce bai ma iya karatun turancin ba.