
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa, cikin sanatoci 106 da ake dasu, guda 87 duk ‘yan APC ne.
Ya bayyana hakane a wajan zaman majalisar inda yace amma da yawa kamar 20 da wani abu a yanzu haka suna son shiga jam’iyyar ta APC amma ana kan tattaunawa dasu.
Yace zai sanar da matsayinsu idan tattaunawar ta kammala.