Thursday, April 23
Shadow

Da Duminsa: DSS sun Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan yiwa wayar me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse

Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar DSS sun gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban kotu saboda zargin yiwa wayar me baiwa shugaban kasa, Shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse.

DSS sun gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne bisa zarge-zarge guda 5 inda a baya suke msa zarge-zarge guda 3.

Saidai Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya musanta duka zarge-zargen da ake masa.

Saidai Lauyan DSS, Oluwole Aladeloye ya nemi a musu shari’a.

Saidai Lauyan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Oluwole Iyamu ya nemi cewa, a dakatar a bashi lokaci ya tattauna da wanda yake wakilta dan ya dade a tsare a hannun jami’an tsaro.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Musulmai 12 dake kan hanyar zuwa wajan Maulidi sun bace a kauyen Zak dake jihar Filato

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *