
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar DSS sun gurfanar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a gaban kotu saboda zargin yiwa wayar me baiwa shugaban kasa, Shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu kutse.
DSS sun gurfanar da malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne bisa zarge-zarge guda 5 inda a baya suke msa zarge-zarge guda 3.
Saidai Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya musanta duka zarge-zargen da ake masa.
Saidai Lauyan DSS, Oluwole Aladeloye ya nemi a musu shari’a.
Saidai Lauyan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Oluwole Iyamu ya nemi cewa, a dakatar a bashi lokaci ya tattauna da wanda yake wakilta dan ya dade a tsare a hannun jami’an tsaro.