Friday, June 26
Shadow

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya aikawa majalisa bukatar ciwo bashin Dala Miliyan $516

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aikawa majalisar Dattijai da bukatar ciwo bashin dala Miliyan $516.

Shugaban ya aika da bukatar ne a yau, Alhamis inda yace za’a yi aikin gina titin Sokoto-Badagry ne da kudaden.

Kakakin majalisar, Godswill Akpabio ya bayyana cewa akwai bukatar a gaggauta amincewa da karbo bashin.

Ya bayyana cewa, ya baiwa kwamitin kula da bashi na majalisar umarnin su kammala amincewa da bashin cikin sati daya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Kasashe da yawa ciki hadda Idiya sun ki amincewa da Jakadun da shugaba Tinubu ya aika musu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *