Monday, April 27
Shadow

Kalli Bidiyon: Haduwar Sowore da Abubakar Malami a kotu, inda Sowore ke cewa Malami kaima kaji yanda ake ji idan ana zaluntar mutum koh

Mawallafin jaridar Sahara reporters, Kuma dan Fafutuka, Omoyele Sowore ya hadu da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami inda yake tambayarsa shima ya ji yanda ake ji koh idan ana zaluntar mutum.

Sowore yace Malami haka ya rikawa mutane a lokacin yana ministan shari’a yanzu shima abin ya zo kansa.

Saidai ya jinjinawa Malami da cewa bai razana ba da abinda ake masa.

Shima Malamin ya mayar masa da raddin cewa, lallai bai tsorata ba dan duk zaman kotun da za’a yi sai ya halarta.

Karanta Wannan  Kamfanin DSTV da sauran tashoshi na Tauraron dan Adam sun tafka asarar Dala Miliyan $158.19 saboda 'yan Najeriya da yawa yanzu sun daina saka kati saboda matsin tattalin arziki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *