Wednesday, January 15
Shadow

Gyaran Gashi

Akwai hanyoyi da yawa na gyaran gashi wanda ba ma sai kin sayi mai ba idan kinso. A wannan rubutu, zamu kawo muku abubuwan gyara gashi daban-daban wanda za’a iya hadawa a gida:

Man Zaitun: Ana samun man zaitun wanda ba’a hadashi da komai ba, a rika amfani dashi wajan gyaran gashi, man zaitun yana taimakawa sosai wajan kara yawan gashi, hanashi karyewa, sa gashi ya rika sheki da sauransu.

Idan gashin kanki ya lalace, ko yana yawan bushewa ko yana kaikai, man zaitun na magance wadannan matsaloli.

Ana shafa man zaitun akai, bayan mintuna 30 sai a wanke ko kuma idan anzo kwanciya sai a shafashi, da safe a wanke da ruwan dumi.

Karanta Wannan  Amfanin albasa a gashi

Man Kwakwa: Bayan Man zaitun, ana kuma amfani da Man Kwakwa wanda ba’a gaurashi da komai ba wajan gyaran Gashi.

Shima ana shafashi zuwa mintuna 30 sai a wanke da ruwan dumi, yana gyara gashi sosai, yana kara girman gashi, yana sa gashi sheki, yana sa gashin yayi laushi da sauransu.

Lemun Tsami: Bayan Man Zaitun, ana kuma amfani da ruwan lemun tsami wajan gyaran kai. Yana maganin dandruff/amosanin kai, yana sa kai sheki, yana fitar da kala daga jikin gashi, yana ragewa gashi maski, a wani kaulin ma yana kara girman gashi.

Ana hana ruwan lemun tsami da ruwa, zuma ko man zaitun a shafa akai, a barshi ya kai mintuna 20 zuwa 30 sannan a wanke da shampoo.

Karanta Wannan  Hadin tsawon gashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *