Friday, June 26
Shadow

Kalli Bidiyon: Ashe Alhassan Ado Doguwa Gwamna Abba ya taba shiyasa aka hanashi takarar kujerarsa a APC

A dazu ne rahotanni suka yi yawa musamman a kafafen sada zumunta cewa, Jam’iyyar APC a jihar Kano, ta hana Alhassan Ado Doguwa takarar kujerar majalisar wakilai.

Lamarin ya zowa mutane da yawa da mamaki ganin cewa ya shafe shekara da shekaru yana rike da wannan kujerar.

Saidai wani Bidiyo ya bayyana a kafafen sadarwa inda aka ji yana sukar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan cewar da yayi Kullu Nafsin Zalikatul Maut.

Doguwa yacw abin kunyane ga jihar Kano a ji Gwamnanta ya fadi irin wannan maganar yana dan musulmi.

Da yawa sun alakanta cewa wannan magana da Alhassan Ado Doguwa yayi ce tasa aka hanashi tikitin tsayawa takarar majalisar wakilansa.

Karanta Wannan  Ina goyon bayan kudirin dokar canja fasalin karba da raba Haraji a Najeriya>>Inji Bishop Kukah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *