Tuesday, May 12
Shadow

Da Duminsa: Wani babban dan siyasa ya fallasa yanda Kwankwaso kewa Shugaba Tinubu aiki a boye

A yayin da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya bayyana tabbacin hadewarsa da Peter Obi inda yace zai masa mataimakin shugaban kasa a takarar 2027.

Rahotanni daga Marali Radio TV sun bayyana cewa, Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya tonawa Kwankwaso Asiri kan yanda yakewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu aiki a boye.

A cewar kafar, Malam Ibrahim Shekarau yace gara su a bayyane sukewa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu aiki, amma shi Kwankwaso ai a boye yakewa shugaban aiki.

Zuwa yanzu dai Kwankwaso bai ce uffan kan wannan zargi ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Buhari ya gama sukar Marigayi 'Yar'adua amma shima gashi a Landan ya rigamu gidan gaskiya>>Inji Malam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *