Friday, June 26
Shadow

A karin farko, ‘yan majalisar wakilai sun murza gashin baki inda suka cewa, shugaba Tinubu ko dai ya dakatar da duk wani shirin siyasa da yakin neman zabe ya magance matsalar tsaro, ko kuma ya sauka kawai

‘Yan majalisar wakilai marasa rinjaye sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dakatar da maganar yakin neman zabensa a 2027 ya mayar da hankali wajan magance matsalar tsaro.

Sun bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai inda suka ce matsalar tsaro ta kai makura a kasarnan inda suka kawo misali da abinda ya faru da janar Rabe Abubakar a jihar Katsina.

‘Yan majalisar sun zargi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da nuna halin ko in kula game da matsalar tsaron inda yafi mayar da hankali wajan yakin neman zabensa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo da Duminsa: A karshe dai Ummi Nuhu ta samu mijin aure, wanda ya fito da gaske yana son aurenta, kaleshi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *