
‘Yan majalisar wakilai marasa rinjaye sun yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dakatar da maganar yakin neman zabensa a 2027 ya mayar da hankali wajan magance matsalar tsaro.
Sun bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai inda suka ce matsalar tsaro ta kai makura a kasarnan inda suka kawo misali da abinda ya faru da janar Rabe Abubakar a jihar Katsina.
‘Yan majalisar sun zargi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da nuna halin ko in kula game da matsalar tsaron inda yafi mayar da hankali wajan yakin neman zabensa.