
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta cire naira Biliyan 500 daga asusun hadakar Gwamnatoci kamin a raba kudaden shigar da aka tare tsakanin Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi.
Wata Majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng cewa lallai an cire kudin wanda aka ware dan ko ta kwana musamman a bangaren tsaro.
Jaridar tace akawun jihohi wanda dasu ake aikin raba wadannan kudade basu yi korafi akan cire wadannan kudade ba wanda hakan ke nuna cewa suna sane da hakan.
A baya ma dai an cire jimullar Naira Biliyan N952bn inda aka baiwa Sojoji, da wasu ma’aikatun Gwamnati da yin ayyukan ci gaba a wasu jihohi.