
Matar Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Asia El-Rufai ta yi zargin cewa an yiwa wayarta data abokiyar zamanta, Aichatou kutse.
Ta bayyana hakane a shafin ta na sada zumunta inda tace suna zargin Gwamnati, Kuma duk abinda ya samesu, gwamnati ce sila.
Ta bayyana cewa an musu kutse ana saka ido akan abubuwan da suke aikatawa.
Hakan na zuwane yayin da mijinsu ke can hannun jami’an tsaro ana tuhumarsa kan zarge-zargen daban-daban.