
Tauraron Fina-finan Hausa, Musbahu M. Ahmad ya bayyana cewa, ba zasu kara lamunta ba duk malamin da ya kara hawa kumbari ya zagesu suma zasu fito su rama.
Ya bayyana hakane bayan da wani malami ya fito yana sukar ‘yan fim.
Musbahu ya kara da cewa, suna zuwa wajan ‘yan siyasar kuma suna gaya musu halayen malaman cewa ‘yan ci da addini ne.