
Abokin Dan Shugaban kasa, Kuma Attajiri daga kudancin Najeriya, Cubana Chief Priest ya sayi motocin Alfarma na Lamborghini Urus, da Rolls Royce ya bayar a yi yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya wallafa Bidiyon motocin da ya siya a kafarsa ta sada zumunta inda lamarin ya dauki hankula.