Sunday, August 16
Shadow

An canjawa DPO din Maraban Jos da ake zargin ya mikawa mafusata Ummulkhairi wurin aiki inda aka mayar dashi Kurmin Mashi, saidai ‘yan uwanguwar sun ce basu yadda ba

Ordinary President, Ahmad Isa yayi zargin cewa an canjawa DPO din maraban jos wajan aiki inda aka mayar dashi unguwar Kurmin Mashi.

Yace mutanen Unguwar Kurmin Mashi ne suka kirashi suka sanar dashi hakan inda suka ce ba zasu yadda ba, zasu fito zanga-zanga.

DPO din dai shine ake zargin ya mika Ummulkhairi Malamar Islamiyya wajan mafusata suka mata aika-aika.

Inda yace ba zasu yadda ba ace ba a binciki DPO din ba kuma ba’a hukuntashi ba ace an canja masa wurin aiki.

Karanta Wannan  Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello da EFCC ke bincike kan zargin Satar Naira Biliyan 80 yace shugaba Tinubu ba sai ya je jikar Kogi yakin neman zabe ba, ya ci zaben 2027 a jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *