
An zargi Tauraruwar fina-finan Hausa, Lulu da fitar da Bidiyon update din wata.
Sannan an zargeta da zuwa ta nuna Bidiyon ga mahaifiyar me Bidiyon, sannan an zargeta da dukan mahaifiyar wadda suke fadan.
I da labarin ke cewa, wai wata daga Amurka ta kira tasa an kamata sannan an mata na jaki.
Bayan watsuwar lamarin a kafafen sada zumunta, Lulu ta fito ta yi karin haske kan lamarin.
Tace duka wancan labarin ba gaskiya bane, bata fitar da Bidiyon update din kowa ba, sannan bata daki mahaifiyar kowa ba sannan ba’a kamata ba hakanan kuma ba’a daketa ba.
Ta yi zargin cewa wasu ne kawai dake neman suna da sunansu suke yada labaran karya akanta amma babu wani abu makamancin hakan da ya faru da ita.
Lulu tace ba halinta bane ta rika fitar da tsiraicin mutane ba.
