Friday, July 24
Shadow

Kalli Bidiyon: Da gaske kudina gaba daya suna hannun Mahaifiyata>>Inji Hakimi

A wata hira da aka yi dashi, An tambayi dan kwallon kasar Morocco, Hakimi ya shin da gaske kudinsa na hannun Mahaifiyarsa?

Sai yace tun da yana karamin yaro ba zai iya bude asusun banki ba, Mahaifiyarsa ce ke ajiye masa kudinsa.

Yace to ko da ya girma ya riga ya saba da hakan, shiyasa kawai bai chanja ba.

Hakimi ya kara da cewa baiwa mahaifiyarsa kudinsa ta ajiye masa bashi da nasaba da aure.

A baya dai da zai rabu da Budurwarsa, Ta nemi a raba kudinsa a bata, amma da aka duba aka ga bashi da komai ashe komi da yake saye da sunan Mahaifiyarsa yake saye.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: An tura jirgin sama ya dauko Ali Jita ya je yayi waka a wajan wani Biki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *