
Kwamishinan ‘yansanda jihar Lagos, Tunji Disu ya halarci wajan taron City Boy Movement wanda taro ne na yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Saidai zuwansa wajan ya jawo cece-kuce sosai.
Inda ake ta Allah wadai da fadar cewa hukumomin tsaro bai kamata suna halartar wajan tarukan goyon bayan ‘yan siyasa ba.
Da yawa sun yi kiran cewa ya kamata a saukeshi daga mukaminsa.