
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Aminu Daurawa ya fayyace gaskiya kan Bidiyonsa da ake yadawa cewa wai ya halatta auren mutu’a.
Da farko dai yace:
Tsokaci kan auran Mutu’a
Auren Mut’ah (auren da ake ɗaura shi na wani ƙayyadadden lokaci) mafi yawan malamai na Ahlus-Sunnah sun yi ittifāƙi cewa haramun ne, saboda an halatta shi na ɗan lokaci a farkon Musulunci, sannan Manzon Allah ﷺ ya haramta shi har zuwa Ranar Alƙiyama.
Daga cikin hujjojin haramcinsa akwai:
- Hadisin Sahih Muslim, inda Annabi ﷺ ya ce:
“Na taɓa ba ku izinin yin auren mut’ah, amma yanzu Allah Ya haramta shi har zuwa Ranar Alƙiyama.”
- Hadisin Ali ibn Abi Talib cewa:
“Manzon Allah ﷺ ya hana auren mut’ah a ranar Khaibar.”
Dalilan haramcinsa
- Ya saɓa da manufar aure a Musulunci wadda ta ginu kan zaman dindindin, soyayya, da gina iyali.
- Yana jawo rikice-rikice wajen nasaba, gado, da haƙƙoƙin ma’aurata.
- Ya buɗe ƙofar amfani da mata ta hanyar da ta yi kama da lalata.
Lura: A fahimtar Ahlus-Sunnah, auren mut’ah ya kasance an halatta shi na ɗan lokaci ne, daga baya kuma aka soke wannan hukuncin, kuma ya kasance haramun har zuwa Ranar Alƙiyama.