Friday, October 2
Shadow

Kalli Bidiyon: Sheikh Uti Da’awah na kasar Ghana yana kuka bayan da Kiristocin kasar suka zargeshi da batanci ba Annabi Isa(AS)

Sheikh Uti Da’awa na kasar Ghana yana fuskantar suka da matsin lamba daga Kiristocin kasar bisa zargin cewa yayi batanci ga Annabi Isa (AS).

Wani Bidiyonsa ya bayyana inda aka ji yana fadar wasu munanan kalamai yana dangantasu ga Annabi Isa (AS).

Hakan yasa Kiristocin ke sukarsa da kira ga jami’an tsaro da su kamashi.

Saidai a nasa jawabin, yace wadannan kalamai yayi su ne shekaru 3 da suka gabata a wajan wata mukabala.

Yace kuma yana fadar irin batancin da ‘yan Ahmadiyya ne suka yi ga Annabi Isa (AS) inda yake kore wannan batancin.

Yace amma bashine ya fadi wadannan kalamai ba, inda ya zargi Kiristocin da bata masa suna.

Karanta Wannan  Ku daure ku sake zaben Tinubu a 2027 ko dan ya kammala ayyukan ci gaban da ya faro a Arewa>>Femi Gbajabiamila shugaban ma'aikatan fadar Tinubu ya roki 'yan Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *