
Wannan wata ‘yar Najeriya ce data je aikatau Dubai.
Bayan ta tafi, ta rika aika kudi cikin asusun ajiyarta na bankin access bank har suka kai Naira Miliyan 3.
Data dawo Najeriya ta je ta cire kudin data tara, sai ta tarar babu ko sisi.
Ashe layinta na MTN, kamfanin MTN sun baiwa wani ya sayeshi a matsayin sabon layi, shine shi kuma da ya ga Alert din kudi na shigowa ta layin, ya rika cire Naira dubu 20 har ya karar da kudin gaba daya