Wednesday, September 23
Shadow

Gwamnatin tarayya ta bayar da lasisin shigo da man fetur ganga 830,000

Gwamnatin tarayya ta bayar da lasisin shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje har ganga 830,000.

Gwamnatin ta bayar da lasisin ne wanda za’a yi amfani dashi a watanni 4 na karshen shekara yayin da za’a shiga bukukuwan karshen shekara.

Hakan na zuwane yayin da ake ci gaba da amfani da man da aka tace a cikin gida da wanda aka shigo dashi daga kasashen waje dan biyan bukatar masu ababen hawa a Najeriya.

Kamfanonin da aka baiwa lasisin shigo da man fetur din sune, AYM Shafa, NIPCO, Pinnacle Oil, Bono Ene3egy, Matrix Energy, da AA. Rano.

Karanta Wannan  Masu wakokin Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Sufayene, Kuma wallahi sunfi son Annabi, amma kun dage sai kun gano Laifinsu>>Sheikh Nura Khalid, Digital Imam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *