Monday, September 28
Shadow

Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar NDC

Rahotanni sun bayyana cewa, Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar NDC bayan da jam’iyyar tace zata fara yin rijistar membobinta kamin zabe.

Me magana da yawun jam’iyyar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yace za’a yi rijistarne kyauta.

Saidai bangarori biyu na jam’iyyar Watau Ok Movement da Kwankwasiyya duk sunce basu yadda ba.

Sun ce ba za’a sakasu cikin wadanda zasu yi rijista a jam’iyyar ta NDC ba.

Shugaban Tafiyar Kwankwasiyya, Habibu Muhammad yace ko da a baya su kunyane basa yin rijistar jam’iyyar dan haka a yanzu ma ba zasu yi ba.

Yace burin dai shine ‘yan takararsu su yi nasara dan haka abinda zasu saka a gaba kenan.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tarayya ta mikawa bankin Duniya kokon barar ciwo bashin dala Biliyan $1.5

Shima shugaban Tafiyar Ok Movement, John Ughulu ya bayyana cewa ba zasu yi rijista da jam’iyyar NDC ba dan doka ta basu damar yin kungiyar goyon bayan dan takara ba tare da yin rijista da jam’iyya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *