Sabuwar rawar da gwamnan Osun, Ademola Adeleke yayi ta dauki hankula a shafukan sada zumunta.
Gwamna Adeleke ya shahara wajan rawa a guraren taruka da yake halarta.
Gwamnan dai kawu ne ga shahararren mawakin Najeriya, Davido.
A wannan karin ma ya sake taka rawar a wajan taron karrama mutane da jaridar Vanguard ta yi.
Kalli Bidiyon a kasa:
Yayin da wasu ke yaba mai, wasu na ganin hakan bai dace ba a matsayinsa na gwamna.