An kama wasu barayi da suka yi yunkurin yin sata a yayin da gobarar garin Los Angeles na jihar California kasar Amurka ke ci.
A yayin da ake neman masu kashe gobara saboda karanci kuma mutane da yawa ke guduwa suna barin gidaje da dukiyoyinsu, wadannan bata gari su kuma sata ce suka sa a gaba.
Zuwa yanzu mutane 4 ne mahukuntan jihar suka fitar da hotunansu a matsayin barayin.
Gobarar dai ta kone gidaje sama dubu goma sha biyu inda masu kashe gobara sama da dubu goma sha hudu ke ta kokarin kasheta.