
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam’iyyar APC ba.
Ya bayyana hakane a wajan taron Jam’iyyar PDP da aka gudamar a Jiya Asabar inda yace masu ruguguwar komawa APC suna yi ne dan neman na Abinci.
Yace ba dan mutane ‘yan siyasar suke komawa APC ba inda yace ta yaya zasu rika saurin komawa Jam’iyyar duk da matsin tattalin arzikin da ake fama dashi da kuma rashin iya mulki na Jam’iyyar.
Yayi kira ga ‘yan Adawa da su hada kai a shekarar 2027 su kawar da Jam’iyyar ta APC daga mulki.