Tuesday, September 8
Shadow

Abinda na gani a rasuwar Zee Diamond yasa na tsani Harkar fim

Allah Dai Ya Ba Mu Mazajen Aure Kawai, Don Wallahi Harkar Fim Ɗin Hausa Ba Sana’a Ba Ce, Saboda Na Yi Mamakin Yadda Ƴan Fim Ba Su Halarci Jana’izar Zee Diamond Ba, Inji Wannan Jaruma

Jarumar ta ƙara da cewa ƴan fim ɗin da suka halarci jana’izar ba su wuce mutum biyar ba, kamar Yusuf Lazio, Darakta Gidaje da Najib marubuci. Sai kuma a mata su uku ne.

Jarumar ta ce duk da cewa marigayiyar ta yi jama’a, amma idan ta ƴan fim ne da saidai ta ruɓe a gida, domin tun wajen ƙarfe 12 na rana suka je gidan rasuwar, amma sai wajen ƙarfe uku aka yi jana’izarta.

Karanta Wannan  Kalli Hoto: Yanda aka kama sojan Najeriya, Yahya Yunusa na safarar makamai a Kaduna

Ta ce a yau ta ƙara tsanar masana’antar fim domin ana amfani da su ne a masana’antar a lokacin da suke da lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *