
Wani matashi ya bayyana yanda ya tafka Asarar Naira Miliyan 2 a Kiwon Kaji.
Yace ya kashe kudi sosai wajan kula dasu da basu magani.
Yace Asali ma wani Likitan kajinne ya bashi waje a gidan gonarsa ya zuba kajin kuma shi ke kula masa da lafiyarsu inda yace likitan na da kwarewa ta tsawon shekaru 15.

Yace amma sai gashi ya tafka asara.
Yace gashi yanzu ana binsa bashin Naira dubu dari takwas, 800k.