
Mutane da aka diba suka je wajan taron yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jihar Enugu an gansu ana sallamarsu da Naira dubu biyar amma sun ce basu yadda ba.
Sun ce babu ta yanda za’a yi tun karfe 9 har zuwa 5 na yamma suna tsaye amma a dauko wata dubu biyar ana basu.
An gansu sun yi cirko-cirko suna shirin lakadawa masu basu kudin na jaki.