
Rahotanni sun bayyana cewa na’urar sanyaya daki, watau AC ta daina aiki a wajan babban taron jam’iyyar ADC sannan an dauke wuta, kamar yanda muka kawo muku a baya.
Hakan yasa dole saidai fankoki aka dauko aka kawo wajan taron.
Bayan da manyan baki suka gama kammaluwa, an ga kowa ciki hadda su Atiku, Kwankwaso, Peter Obi, Rotimi Amaechi sai fifita suke.