Wednesday, October 14
Shadow

Allah yawa Me kiran Sallah na masallacin Makkah Rasuwa

Rahotanni daga kasar Saudiyya na cewa, Allah yawa me kiran Sallah na masallacin Makkah, Sheikh Ibrahim Adel Al-Madani rasuwa.

An haifeshi a shekarar 1397 bayan Hijira, wadda za’a iya cewa a shekarar 1976 a shekarar bature, a garin Madina, kuma kakansa mahaddacin Qur’ani ne wanda hakan yayi tasiri sosai a rayuwarsa.

Ya fara kiran sallah yana da shekaru 15 a masallacin Unguwarsu kuma ya ci gaba har ya kammala jami’a.

A shekarar 1439 bayan Hijira ne aka nadashi a matsayin me kiran Sallah na masallacin Makkah.

Ya rasune da safiyar yau 11 Rabi Al Thani 1448.

Muna fatan Allah ya jikansa da Rahama.

https://twitter.com/MakkahUpdate/status/2101890875202637855
Karanta Wannan  Malamin Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ya Rasu Yana Tsakar Sallar Tarawih

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *