Wednesday, January 15
Shadow

Amfanin bawon kwai

Bawon kwai yana da amfani sosai a jiki wanda idan kasan amfaninsa, daga yau ba zaka kara yadda shi a bola ba.

Hakan zai rage dattin da ake tarawa a dakin girki.

Ko kunsan cewa, bawon kwai yana bayar da abinda ake cewa Calcium wanda sinadarine dake kara karfin kashi da hakora wanda ke baiwa mutum kuzari sosai.

Ana yin garin danyen kwai a rika hadawa da abinci ko a yi kamar shayi a rika sha.

Masana kiwon lafiya sun ce, rabin bawon kwai yana dauke da sinadarin Calcium da babban mutum ke bukata a kowace rana. Watau idan mutum zai ci rabin bawon kwai a rana ya isheshi ya samu karfin hakori da na kashi da ake bukata ya samu a ranar.

Karanta Wannan  Amfanin toka a hammata

Hakanan masana kiwon lafiya sun kara da cewa, Bawon kwai yana dauke da Calcium fiye da duk wani Calcium da mutum zai samu a wani abu da aka hada.

Hakanan bawon kwai yana taimakawa karfin kashi da kuma hana ko rage hadarin karaya insha Allah.

Wanda ke fama da rashin kwarin kashi wanda yawanci tsufa ke kawoshi ko kuma ko da matashine dake fama da rashin kwarin kashi zai iya amfani da bawon kwai, yana amfani sosai in Allah ya yarda.

Hakanan ina wannan farar fatar dake jikin soyayyen kwai bayan an dafa? Wadda wani lokacin zata makale a jikin kwai din ko kuma ta makale a jikin bawon kwan,itama tana da matukar amfani sosai wajan kara karfin kashi,a daina bareta idan ana bukatar sinadarin Calcium.

Karanta Wannan  Maganin daina luwadi

Abubuwan da za’a kiyaye idan ana son amfani da bawon kwai:

Masana kiwon lafiya sun ce a yi amfani da bawon kwai wanda aka dafa, watau bayan an tafasa kwai din ya dahu daidai ci, to irin wannan bawon kwan aka fi son amfani dashi.

Dalili kuwa shine tafasawar tana kashe kwayoyin cutar dake jikin bawon kwan.

Hakanan kada a ce za’a rika cin bawon kwan kai tsaye. An fi son a dakashi a mayar dashi hoda a rika sha a shayi ko a ci a abinci kamar yaji.

Yana da kyau kada a ce za’a rika shan wannan hodar kullun ko da yawa sosai dan duk abinda aka yishi fiye da kima, zai iya bayar da matsala.

Karanta Wannan  Maganin yawan tusa

Neman shawarar Likita zai taimaka wajan amfani da bawon kwai

Allah ne mafi sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *