
Rahotanni daga jihar Osun na cewa, tsohon shugaban karamar hukumar Irewole, Mr. Aderemi Abbas da wasu mutane 6 sun mutu bayan da rikicin siyasa ya barke a jihar.
Rikicin ya barkene bayan da kotu ta tabbatar da shuwagabannin kananan hukumomi da kansiloli na Jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka lashe zabe a jihar.
A baya dai,Gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya kwarmata cewa minista Adegboyega Oyetola wanda tsohon gwamnan jihar ne na son tayar da rikici a jihar bosa goyon bayan jami’an tsaro.
Rahoton jaridar Punchng ya bayyana cewa wani jami’in tsaro dake tsaye kusa da gawar Abbas ya bayyana cewa tsohon shugaban karamar hukumar ya mutu ne a yayin da rikici ya barke tsakanin ‘yan siyasar.
Rahoton yace a ranar Litinin an samu tashe-tashen hankula a kananan hukumomi daban-daban dake fadin jihar inda wasu suka mutu wasu suka jikkata.
Tuni dai shugaban ‘yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya aike da Karin jami’ai jihar.