
Dattijo a yankin Neja Delta da ke kudancin Najeriya kuma tsohon kwamashina, Edwin Clark, ya rasu yana da shekara 97 da haihuwa.
A cewar wata sanarwa da kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito daga iyalinsa, tsohon shugaban ƙungiyar rajin kare yankin Neja Delta ta Pan Niger Delta Forum (PANDEF) ya rasu ranar Litinin da dare.
“Mutumin da aka haifa a Kiagbodo da ke yankin Ijaw na jihar Delta, Clark ya yi aiki tare da gwamnan mulkin soja Samuel Ogbemudia, da Janar Yakubu Gowon tsakanin shekarun 1966 zuwa 1975,” a cewar sanarwar.
Ya riƙe muƙamin kwamashinan yaɗa labarai a shekarar 1975.