Da Duminsa: ‘Yan Bìnďìgà sun sake kaiwa wutar lantarkin Najeriya hari
Rahotanni daga jihar Kogi sun bayyana cewa, 'yan Bindiga sun sake kaiwa tashar wutar lantarki da hukumar TCN ke kan ginawa hari.
Tashar wutar lantarkin tana garin Obajanane.
Me kula da yada labarai na kamfanin, Ndidi Mbah ne ya tabbatar da hakan inda yace an kai harinne da daren ranar Talata.
Jami'an tsaron dake gadin tashar wutar sunce maharan na zuwa suka bude wuta suna harbin kan mai uwa da wabi wanda hakan yasa suka tsere.
TCN tace a yanzu tana bincike dan ganin irin girman barnar da maharan suka yi.