Friday, July 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Dangote ya zarta Kasar Amurka wajan yawan man jirgin sama da ake kaiwa zuwa kasashen Turai

Dangote ya zarta Kasar Amurka wajan yawan man jirgin sama da ake kaiwa zuwa kasashen Turai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, matatar man Dangote ta zarta kasar Amirka wajan kai man jiragen sama kasashen Turai a wajan Yuni daya gabata. A watan Yunin da ya gabata, Matatar man ta Dangote ta kai Man jirgin sama Ganga 466,000 zuwa kasashen Turai wanda darajarsa ya kai Naira Biliyan N757bn. Amma yawan wanda kasar Amurka ta kai kasashen Turan bai kai haka ba. Wannan ba karamin ci gaba bane ga Dangoten dama Najeriya baki daya.
Kalli Bidiyon: Tauraruwar Tiktok ta rigamu gidan gaskiya, rasuwarta ta girgiza mutane sosai

Kalli Bidiyon: Tauraruwar Tiktok ta rigamu gidan gaskiya, rasuwarta ta girgiza mutane sosai

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok me suna Hadiza ta rigamu gidan gaskiya. Matashiyar ta shahara a Tiktok inda takan dora Bidiyon irin dai wanda 'yan mata ke dorawa. Koda a ranar da zata rasu, ta dora Bidiyon awanni 24 da suka gabata. Na kusa da ita sun bayyana kaduwa da rasuwarta inda suka bayyana ta a matsayin mutuniyar kirki. https://www.tiktok.com/@fahadkabirmaitata/video/7659178916569107733?_r=1&_t=ZS-97ndbfVZApE
Kalli Bidiyon: Rarara, Kwatankwacin Annabi Isa ne, Busawa mutane rai yake, Inji Tauraron fina-finan Hausa, Razaki Dadin Kowa

Kalli Bidiyon: Rarara, Kwatankwacin Annabi Isa ne, Busawa mutane rai yake, Inji Tauraron fina-finan Hausa, Razaki Dadin Kowa

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Razaki Dadin Kowa ya bayyana cewa, Tauraron mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, Busawa mutane Numfashi yake, Subhanallah. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi inda har ya kawo misali da wani da ya rame sai saura fata a jikinsa amma Rarara ya busa masa numfashi. Ya soki masu fita daga tafiyar rararata neman shugaba Tinubu ya zarce. https://www.tiktok.com/@razaki_dadinkowa/video/7659073695427693845?_r=1&_t=ZS-97n3ES2TKX2
Kalli Bidiyon: Na samu damar barin Najeriya, zan koma kasar Switzerland da zama>>Inji Y America

Kalli Bidiyon: Na samu damar barin Najeriya, zan koma kasar Switzerland da zama>>Inji Y America

Duk Labarai
Shahararren me yada badala a Tiktok, Y America ya bayyana cewa, zai bar Najeriya zuwa kasar Switzerland. Y America ya bayyana hakane a wani Bidiyo daya wallafa a shafinsa na Tiktok inda yace zai koma can Turai dan ci gaba da mu'amala da matan Turawa. Yace wanda yake ganin shine matsalarsa a Najeriya to zai gani idan ya tafi. https://www.tiktok.com/@y834097/video/7658722815675223310?_r=1&_t=ZS-97n24IHUzsV
Wannan matashiyar data gudo daga Bakori Jihar Katsina ta je Kaduna tace wai Kishiyar Mahaifiyarta na sata bun maza ashe karya take

Wannan matashiyar data gudo daga Bakori Jihar Katsina ta je Kaduna tace wai Kishiyar Mahaifiyarta na sata bun maza ashe karya take

Duk Labarai
Wannan matashiyar ta dauki hankula a kafafen sada zumunta sosai bayan da ta bayyana inda tace daga garin Bakori na jihar Katsina ta fito. Tace dai wai kishiyar mahaifiyarta ce ke sata bin maza saboda ita Mahaifiyar ta ta rasu sannan tana sakata Tallah. Dan hakane ma yasa ta tsere. Saidai a yanzu Mahaifinta ya bita zuwa Kaduna inda ya bayyana cewa karya take tana da aure ma kuma mahaifiyar ta na nan da rai. Mahaifin yace ba auren dole yawa diyar tasa ba. https://www.tiktok.com/@bappah28/video/7658704598974139656?_r=1&_t=ZS-97n0w2HC0PA