Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Subhanallah Kalli Bidiyon: An kara samun wani matashi da yayi ridda ya koma Kirista a jihar Borno

Subhanallah Kalli Bidiyon: An kara samun wani matashi da yayi ridda ya koma Kirista a jihar Borno

Duk Labarai
Wani matashi ya yi ridda ya koma Kirista a jihar Borno. Bidiyon matashin ya yadu sosai a kafafen sadarwa inda ake ta mayar da raddi, wasu na zargin baya cikin hayyacinsa yayi hakan. Hakan na zuwane yayin da ake tsaka da jimamin matashi Abdullahi dan jihar katsina wanda shima yayi ridda ya koma kirista. https://www.tiktok.com/@mohammedmhammed76/video/7561152764986871047?_t=ZS-90ZZUeOIkxF&_r=1
Kalli Bidiyo: Ba laifi bane a haddace wakokin Soyayya a rika Rerawa>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Kalli Bidiyo: Ba laifi bane a haddace wakokin Soyayya a rika Rerawa>>Inji Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Duk Labarai
A wata muryar wa'azinsa da aka ji ta yadu sosai a kafafen sada zumunta, an ji malam Aminu Ibrahim Daurawa na fadar cewa, ba laifi bane a rika sauraren wakar soyayya. Malam yace ana iya sauraren wakar soyayya har a haddace ta. Yace kuma idan mutum na gida zai iya rika rerawa matarsa. https://www.tiktok.com/@ibrahimmaitafsir/video/7560569947840204050?_t=ZS-90ZYbYM8cca&_r=1
Kalli Bidiyo: Wannan ‘yar Najeriyar da ta je aiki kasar Ingila tace abinda ke bata takaici da kasar Ingila shine su kyakkyawar mace bata damesu ba

Kalli Bidiyo: Wannan ‘yar Najeriyar da ta je aiki kasar Ingila tace abinda ke bata takaici da kasar Ingila shine su kyakkyawar mace bata damesu ba

Duk Labarai
Wata matashiya 'yar Najeriya data je aiki a kasar Ingila ta bayyana cewa, ita abinda ke mata takaici da kasar Ingila shine ba ruwansu da wai kina da kyau. Tace duk kyan mace saidai ki yi aiki ki samu kudi amma babu wanda zai baki kudi kawai dan kina da kyau, ba irin Najeriya ba. https://www.youtube.com/watch?v=Ealw73w4iew?si=pcO2Al6KPikb5M78
Dangote ya samu Naira Biliyan 600 a rana daya kacal, Kuma Matsayinsa ya karu a tsakanin masu kudin Duniya

Dangote ya samu Naira Biliyan 600 a rana daya kacal, Kuma Matsayinsa ya karu a tsakanin masu kudin Duniya

Duk Labarai
Dangote ya kama hanyar zama dan Afrika na farko da zai mallaki Zunzurutun kudade har dala Biliyan $30. Rahoton jaridar Bloomberg yace Kudaden Dangote sun kari da dala Miliyan $401 a rana daya wanda shine kwatankwacin Naira Biliyan N601. Hakan yasa yawan kudaden da ya mallaka suka karuwa zuwa Dala Biliyan 29.6. Hakan yasa matsayin Dangote ya karu a tsakanin masu kudin Duniya inda a yanzu yake a mataki na 76
Shugaba Tinubu ya san Kuna cikin wahalar Rayuwa amma kwanannan zata kare>>Inji Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Shugaba Tinubu ya san Kuna cikin wahalar Rayuwa amma kwanannan zata kare>>Inji Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana sane da irin halin matsin rayuwar da ake ciki. Saidai yace abin ya kusa zuwa karshe dan kwanannan lamura zasu gyaru sosai. Ya bayyana hakane a wajan wani taron makamashi da aka gudanar a Abuja ranar Talata 'Yan Najeriya da yawane ke kokawa da matsin rayuwa tun bayan hawan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Mulki a shakarar 2023.
Matar mawakin Amurka, AKON ta nemi su rabu inda ta nemi ya biyata Yuro Miliyan €100, saidai dala Dubu goma($10k) kadai aka iske a asusun ajiyarsa

Matar mawakin Amurka, AKON ta nemi su rabu inda ta nemi ya biyata Yuro Miliyan €100, saidai dala Dubu goma($10k) kadai aka iske a asusun ajiyarsa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, matar shahararren mawakin Amurka, Akon ta nemi ya saketa bayan da suka shafe shekaru 29 da aure. Matar ta nemi ya biyata Yuro Miliyan €100 daga cikin kudin Mawakin. Saidai rahotanni da ba'a tabbatar dasu ba sun ce Dala 10k kadai aka iske a asusun mawakin, saboda sauran kudadenshi duk suna hannun Mahaifiyarsa.
Kalli Bidiyo: Sufayene suka hada kan Musulmai, Wahabiyawa suka raba>>Inji Sheikh Nura Khalid

Kalli Bidiyo: Sufayene suka hada kan Musulmai, Wahabiyawa suka raba>>Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, Sufayene suka Hada kan Musulman Duniya wanda sai da aka shekara 800 da Khalifanci amintacce. Yace Amma da aka tashi raba kan musulmai sai aka kirkiri Wahabiyawa. Yace dasu ne aka yi amfani aka raba kan musulmai. Malam yace kuma kasar Ingila ce ta kirkiresu. https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7560201522907319559?_t=ZS-90ZAcWHuIj3&_r=1
Duk da Gwamnati na karyatawa, Amma ta tabbata cewa, an fitar da Ministan Kudi, Wale Edun da ya kwanta rashin lafiya zuwa kasar waje

Duk da Gwamnati na karyatawa, Amma ta tabbata cewa, an fitar da Ministan Kudi, Wale Edun da ya kwanta rashin lafiya zuwa kasar waje

Duk Labarai
Jaridar Punchng ta ce ta samu tabbacin cewa an fitar da ministan kudi, Wale Edun zuwa kasar Ingila dan neman magani bayan da ya kwanta rashin Lafiya. Ministan dai ya kwanta rashin lafiya wanda rahotannin farko suka ce Shanyewar rabin jiki ce amma daga baya, Fadar shugaban kasa ta musanta hakan. Sannan fadar shugaban kasar tace lallai bashi da lafiya amma ba shanyewar rabin jiki bace, sannan kuma ba'a fitar dashi zuwa kasar waje ba. Amma jaridar Punchng tace tabbas ta samu sahihin labarin da yace mata An fitar da ministan. Hakanan rahotanni sun ce shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon ministan Kudin amma fadar shugaban kasar ta karyata hakan.
Kalli Bidiyo: Aika ‘yan Shi’a Lakhira da sojoji suka yi a Zaria, a mulkin Buhari, da gangan aka yi, babu wata maganar tare hanya, Abune wanda aka shirya da gangan>>Inji Datti Baba Ahmad

Kalli Bidiyo: Aika ‘yan Shi’a Lakhira da sojoji suka yi a Zaria, a mulkin Buhari, da gangan aka yi, babu wata maganar tare hanya, Abune wanda aka shirya da gangan>>Inji Datti Baba Ahmad

Duk Labarai
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Datti Baba Ahmad, ya bayyana cewa, Kashye 'yan Shi'a da aka yi a Zaria wanda sojoji suka yi da cewa wai sun tarewa shugaban sojoni hanya ne shiri ne. Yace abune wanda aka shirya dan cimma wata manufa. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Ya ce kuma yana da hujjoji kan duk wani ikirari da yayi. https://twitter.com/MgajiInnocent/status/1978197067718685129?t=G8CdwXyaB1onQaNfC-9Gcg&s=19