Sunday, December 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

An kori wata malamar coci daga cocin saboda tace ta musulunta, saidai tace karyane, ba dalilin kenan ba, An nemi a mayar da ita Qaruwar cocinne, ana nemanta da lalata taki yadda shiyasa suka koreta

An kori wata malamar coci daga cocin saboda tace ta musulunta, saidai tace karyane, ba dalilin kenan ba, An nemi a mayar da ita Qaruwar cocinne, ana nemanta da lalata taki yadda shiyasa suka koreta

Duk Labarai
Wata malamar coci me suna Annastasia Kinse wadda 'yar Asalin jihar Filato ce dake a matsayin malamar cocin Katolika dake jihar Edo tace an koreta daga aiki ne saboda ta ki yadda ta zama karuwa a cocin kowa ya rika nemanta. Ta bayyana hakane a hirar da aka yi da ita a jaridar Punchng. Kinse itace reverend sister ta farko a kauyensu kuma tana aiki da jami'ar Veritas University sannan tana karatun digiri na biyu, watau Masters a jami'ar Abuja kamin a koreta daga aiki. Tace a shekarar 2015 ne ta shiga aikin cocin kuma ta y aiki da cocin na tsawon shekarau 2 kamin ta samu kwarewa. Tace a watan July na shekarar 2025 ne aka fitar da takardar cewa an koreta daga cocin saboda ta koma musulma, amma ace karyane saboda ta kai karar nemanta da lalata da aka yi n yasa aka koreta. Tace t...
Kalli Bidiyo: Masu kudi na Allah da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) basu wuce mutane 20 ba a Najeriya, Sauran duk barayine>>Inji Ordinary President

Kalli Bidiyo: Masu kudi na Allah da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) basu wuce mutane 20 ba a Najeriya, Sauran duk barayine>>Inji Ordinary President

Duk Labarai
Ahmad Isa, Ordinary President ya bayyana cewa, a Najeriya masu kudi na Allah da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) basu wuce mutane 20 ba. Yace sauran duk Barayine. Ya bayyana cewa, yasan zai yi bakin jini amma zai fada saboda yasan gaskiya idan bai fada ba ya taimakawa zalinci. https://www.tiktok.com/@3star.jr/video/7556671494181391672?_t=ZS-90StGdJRFOC&_r=1
Masu wakokin Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Sufayene, Kuma wallahi sunfi son Annabi, amma kun dage sai kun gano Laifinsu>>Sheikh Nura Khalid, Digital Imam

Masu wakokin Yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Sufayene, Kuma wallahi sunfi son Annabi, amma kun dage sai kun gano Laifinsu>>Sheikh Nura Khalid, Digital Imam

Duk Labarai
Malamin addinin Islama, Sheikh Nura Khalid ya bayyana cewa, Sufayene ke wakokin yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam). Yace amma wanda basa yi sun sasu gaba sai sun gano inda suke kuskure. Yace duk wanda ya dauki littafin wani yana neman kuskure to zai ga kuskuren, saidai ya nemi a shafawa masu yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Lafiya. https://www.tiktok.com/@shaaweuei5p/video/7559703374237584658?_t=ZS-90TqKDQcfVQ&_r=1
EFCC ta kama Mamud Nasidi da Yahaya Nasidi a filin jirgin sama na legas da zunzurutun kudade har dala $6,180 da da fan £53,415

EFCC ta kama Mamud Nasidi da Yahaya Nasidi a filin jirgin sama na legas da zunzurutun kudade har dala $6,180 da da fan £53,415

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama Mamud Nasidi da Yahaya Nasidi, bisa kin bayyana makudan kudaden da suke dauke dasu da suka kai dala $6,180 da da fan £53,415 a filin jirgin sama na Legas. Jami'an kula da filin jirgin saman, (FAAN) ne suka kama masu laifin inda suka damkasu hannun EFCC. Tuni EFCC ta sanar da cewa ta fea bincike kan wadanda ake zargin. Wadanda ake zargin sun zo ne daga Dubai inda suke shirin wucewa zuwa Abuja. An kuma kwace wayoyi guda 3 daga hannunsu.
Jirgin saman ‘yan Kwallon Najeriya, Super Eagles yayi saukar gaggawa bayan da gilashin jirgin ya fashe

Jirgin saman ‘yan Kwallon Najeriya, Super Eagles yayi saukar gaggawa bayan da gilashin jirgin ya fashe

Duk Labarai
Jirgin saman da 'yan kwallon Najeriya, Super Eagles ke ciki yayi saukar gaggawa bayan da gilashin gaba na jirgin ya tsage. Jirgin ya saukane a kasar Angola. 'Yan wasan na dawowa ne daga wasan da suka buga da Lesotho wanda suka yi nasara 2-1. Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, (NFF) ta tabbatar da hakan inda tace direban jirgin yayi kokari sosai wajan saukar da jirgin bayan faruwar lamarin.
Kalli Bidiyon: Ku daina min kallon Mutuniyar Banza, ni ba Qaruwa bace, kuma bana shaye-shaye, neman sunane kawai na fito yi>>Inji Matashiyarnan ‘yar Legas da tace zata Aikata Alfasha da maza 100 dan ta shiga kundin Tarihin Duniya

Matashiyar nan 'yar legas wadda ta fito tace zata aikata Alfasha da maza 100 dan shiga kundin tarihin Duniya ta bayyana cewa ita ka Qaruwa bace. Tace kuma bata shaye-shaye, wiywiy kawai take dan zuqa daga lokaci zuwa lokaci. Matashiyar da aka fi sani da sunan Mandy Kiss tuni Gwamnatin jihar Legas ta bata jakadancin yaki da miyagun kwayoyi. https://twitter.com/whatsappblog9ja/status/1977228790133629308?t=RIUqk16_u4Oganp0Zy4ybQ&s=19
Ya dauke ta ya kai ta gidansa suka kwana da Alkawarin Zai bata Naira dubu dari da hamsin, saidai ya mata Alert din karya(Fake) alert, tana ta kuka

Ya dauke ta ya kai ta gidansa suka kwana da Alkawarin Zai bata Naira dubu dari da hamsin, saidai ya mata Alert din karya(Fake) alert, tana ta kuka

Duk Labarai
Wannan wata me zama kanta ne da rahotanni suka ce wani ya dauketa ya kaita gida suka kwana da niyyar cewa, zai bata Naira 150k amma sai ya mata alert din karya. Ya fice daga inda suka kwana, daga baya data gani ta yi ta kuka. Tuni akaita watsa labarinta a kafafen sada zumunta ana ta muhawara.
Dan Kiripto ya aika kansa Lahira bayan Tafka mumunar Asara biyo bayan lalacewar kasuwar

Dan Kiripto ya aika kansa Lahira bayan Tafka mumunar Asara biyo bayan lalacewar kasuwar

Duk Labarai
Rahotanni sun ce wani dan kasuwar Kiripto me suna Konstantin Ganich ya khashe kansa bayan da ya tafka mummunar Asara. Kasuwar Kiripto ta tafka asarar da ba'a taba ganin irin ta ba data kai ta dala Biliyan 19. Rahotanni sunce a gano gawar mutuminne a cikin motarsa ranar Juma'a. Kasar Ukraine na daya daga cikin kasashen da suka rungumi harkar Kiripto musamman saboda matsin tattalin arzikin da kasar ke fama dashi.
Saidai idan mu duka za’a kama amma abinda Malam Lawal Triumph ya fada duk Ahlussunnah akan shi muke>>Inji Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau

Saidai idan mu duka za’a kama amma abinda Malam Lawal Triumph ya fada duk Ahlussunnah akan shi muke>>Inji Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau

Duk Labarai
Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa, duka 'yan Izala suna kan irin maganar da Malam Lawal Triumph ya fada. Ya jawo hankalin Gwamnatin Kano da cewa, Kada ta siyasantar da harkar Addini. Yace idan kuwa an ce za'a rika kama masu irin wannan ra'ayi to saidai idan kowa da kowa mutanen Ahlussunah za'a kama. https://www.tiktok.com/@dadee308/video/7559618850321337607?_t=ZS-90SUktqxYtl&_r=1