Abubuwan da Tinubu ya faɗa a taron ƙasashen Musulmi kan yaƙin Gaza
Shugaba Bola Tinubu na cikin manyan shugabannin da suka isa Riyadh babban birnin Saudiyya domin halartar taron ƙoli na ƙasashen Musulmi da Larabawa.
Taron wanda aka a fara a yau Litinin 11 ga watan Nuwamba, zai mayar da hankali ne kan rikicin da ake fama da shi a Gabas Ta Tsakiya.
Tinubu ya samu tarba daga tawagar gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin matamakin gwamnan Riyadh, Mohammed Abdurrahman.
Shugaba Tinubu a bayanin da ya yi a gaban taron ya yi kira da a kawo ƙarshen hare-haren Isra'ila a Gaza, inda ya yi gargaɗin cewa " an kwashe lokacin mai tsayi ana wannan rikici kuma hakan ya haifar da wahalhalun da ba za su ƙirgu ba."
Ka zalika ya nuna damuwa kan matsalar kayan agaji a rikicin na Gabas ta Tsakiya.
"A matsayinmu na wakilai daga ƙasashen da suke mutunta adalci da...