Da Duminsa: An kama Direban da ya tuka Dan Damben Najeriya, Anthony Joshua da abokansa suka yi Khàdàrì
Rahotanni sun bayyana cewa, An kama Direban da ya tuka motar su Dan Damben Najeriya, Anthony Joshua da abokansa wanda ta yi hadari.
An kamashi ne aka kaishi ofishin 'yansanda inda aka masa tambayoyi.
Rahotanni sun ce, direban me suna Kayode Adeniyi, dan kimanin shekaru 46 za'a gurfanar dashi ne gaban kotu inda akw zarginsa da aikata laifuka 2 wanda suka hada da tukin ganganci da Kisan kai.
Abokan Anthony Joshua 2 ne suka mutu a wannan hadari wanda shi kuma ya jikkata.








