Thursday, December 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

ADC ta zargi APC da shirin tafka maguɗi a zaɓen cike gurbi na Kaduna

ADC ta zargi APC da shirin tafka maguɗi a zaɓen cike gurbi na Kaduna

Duk Labarai
Kafin zaɓen cike gurbi da za a gudanar a gobe, rnanar Asabar a majalisun tarayya da na jiha a Jihar Kaduna, jam’iyyar adawa ta African ADC ta zargi jam’iyyar mai mulki ta APC da daukar ’yan daba da kuma karɓar biliyoyin naira daga cikin jihar da wajen ta domin yin magudi. Zaɓen cike gurbin zai gudana ne a mazaɓar tarayya ta Chikun/Kajuru da mazaɓar tarayya ta Zaria/Kewaye, da kuma mazaɓar majalisar jiha ta Basawa. Waɗannan zarge-zargen na ADC sun haifar da musayar maganganu tsakaninta da gwamnatin jihar da kuma jam’iyyar APC. Kwamishinan ƴaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki da ya mayar da martani yana cewa zarge-zargen na ADC “ba su da tushe kuma abin dariya ne.”
Tinubu ya naɗa sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

Tinubu ya naɗa sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA

Duk Labarai
Tinubu ya naɗa sabon shugaban gidan talabijin na ƙasa, NTA Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi babban sauy-sauye na shugabanci a gidan talabijin na ƙasa, NTA, inda ya naɗa Rotimi Richard Pedro, a matsayin sabon Darakta-Janar na gidan talabijin din na gwamnati. “Sauran manyan nade-naden sun haɗa da Karimah Bello daga Jihar Katsina a matsayin Daraktar Tallace-Tallace, Stella Din daga Jihar Filato a matsayin Daraktar Labarai, da kuma Sophia Issa Mohammed daga Jihar Adamawa a matsayin Babbar Darakta ta Kamfanin NTA Enterprises Limited. “Pedro, ɗan asalin Legas, fitaccen mai kasuwanci a fannin kafafen watsa labarai da kuma mai ba da shawara, wanda ke da kusan shekaru talatin na kwarewar jagoranci a harkar watsa shirye-shirye, wasanni, da kuma tallace-tallace a faɗin Afirka, Birta...
Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Duk Labarai
Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta kuma kai tsaye ga gidajen mai a Najeriya daga yau, matakin da ake sa ran zai kawo sauyi a harkar man fetur ta ƙasar. Kamfanin ya ce wannan shirin zai rage yawan masu shiga tsakani ya kuma ƙara inganci, tare da bai wa masu amfani da kuma gidajen mai damar samun zaɓuɓɓuka masu rahusa. Matatar man Dangote dai mai ƙarfin tace ganga 650,000 na mai a rana ta fara aiki ne a shekarar 2023, inda ta taimaka wajen rage farashi bayan tashin gwauron zabin da ya biyo bayan cire tallafin mai da shugaba Tinubu yayi.
A biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati – ASUU

A biya mu haƙƙoƙinmu, ba mu son bashin gwamnati – ASUU

Duk Labarai
Ƙungiyoyin ma'aikatan manyan makarantun Najeriya na ci gaba da yin watsi da sabon shirin da gwamnatin tarayyar kasar ta ɓullo da shi domin inganta jin dadin ma'aikata, da haɓaka ƙwarewar aiki, ga ma'aikatan manyan makarantun ƙasar. Ita dai gwamnatin Najeriyan ta ƙaddamar da wani sabon shiri wanda aka tsara zai bayar da bashin kudi har naira miliyan 10 ga ma'aikatan manyan makarantun ƙasar da suka haɗa da na jami'a da kwalejin kimiyya da fasaha da kuma kwalejin ilimi. To sai dai ƙungiyoyin ma'aikatan na ganin cewa ba hanyoyin samar da bashi gare su ya kamata gwamnatin ta ɓullo da su ba a wannan lokaci da ake ciki.
MAAN ta nemi taimakon EFCC, DSS da ƴansanda wajen karɓo bashin da manoman masara su ka karba

MAAN ta nemi taimakon EFCC, DSS da ƴansanda wajen karɓo bashin da manoman masara su ka karba

Duk Labarai
MAAN ta nemi taimakon EFCC, DSS da ƴansanda wajen karɓo bashin da manoman masara su ka karba. Kungiyar Masu Noman Masara ta Najeriya (MAAN) ta ce ta na haɗa gwiwa da DSS, EFCC da ‘yansanda domin dawo da rancen shirin Anchor Borrowers da aka bai wa manoma tsakanin 2018 zuwa 2021. Shugaban MAAN na ƙasa, Bello Abubakar, ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce yawancin manoman da suka karɓi kuɗin sun ki biyan bashin, suna ɗaukar sa a matsayin “kudin al’umma.” Ya ce ƙungiyar ta tura wasikun tuni, ta kuma kai ƙara ga wasu masu bashi, yayin da ake ci gaba da shari’o’i a kotu. Abubakar ya bayyana cewa matsalar tsaro da ambaliyar ruwa na barazana ga noman masara a jihohi da dama, yayin da fari ya shafi wasu yankuna. Ya roƙi gwamnatin tarayya ta samar da yanayi mai...
Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa da su zabi ADC a zaɓukan cike-gurbi

Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa da su zabi ADC a zaɓukan cike-gurbi

Duk Labarai
Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour, Peter Obi ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri'a a Najeriya, musamman masoyansa na ƙungiyar Obidient da su zaɓi jam'iyyar ADC ne a zaɓukan cike gurbi da za a yi a gobe Asabar. Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, "a game da zaɓukan da za a yi a gobe Asabar, 16 ga watan 2025 domin cike gurbin wasu kujeru a jihohi 16 na Najeriya, tunda jam'iyyar LP ba ta da ƴantakara saboda kotu ta hana sanadiyyar rikice-rikicen da ke cikin jam'iyyar, ina kira ga masoyana da su su zaɓi jam'iyyar haɗaka ta ADC a jihohinsu." Wannan jawabin na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara game da yunƙurin haɗakar siyasa, inda ake tunanin manyan jam'iyyun hamayya za su iya haɗuwa a guri ɗaya domin fuskantar Tinubu a zaɓe mai zuwa. ...
Hukumomin Shari’a Sun Amince Da Naira Dubu 20 A Matsayin Mafi Karancin Sadaki

Hukumomin Shari’a Sun Amince Da Naira Dubu 20 A Matsayin Mafi Karancin Sadaki

Duk Labarai
Hukumomin Shari'a Sun Amince Da Naira Dubu 20 A Matsayin Mafi Karancin Sadaki. Hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano tare da Hukumar Shari’a, Majalisar Malamai, Kungiyar Limaman Masallatan Juma’a da Kungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Kasa sun amince da sabbin ka’idoji kan Nisabin Zakka, Diyyar Rai da Sadakin Aure a jihar. A taron da aka gudanar a Kano ranar Alhamis, an yanke shawarar amincewa da naira dubu 20 a matsayin mafi ƙarancin sadakin aure, naira miliyan 150 a matsayin diyya ga wanda aka kashe bisa kuskure, da kuma naira dubu 985 a matsayin nisabin zakka, bisa lissafin farashin Durham. Babban Sakataren Kungiyar Ma’aikatan Zakka da Wakafi ta Kasa, Farfesa Aliyu Tahiru Muhammad na Jami’ar Bayero Kano ne ya bayyana cewa taron ya kuma amince a ci gaba da gudanar da irin...
Da Duminsa: A karin farko, Musulma me sanye da Hijabi, Ameera Hashwi, ta zama Sarauniyar kyau a kasar Amurka

Da Duminsa: A karin farko, Musulma me sanye da Hijabi, Ameera Hashwi, ta zama Sarauniyar kyau a kasar Amurka

Duk Labarai
Matashiya, Ameera Hashwi me shekaru 25 ta zama Sarauniyar kyau ta garin Wayne County, Michigan kasar Amurka. Ta kafa tarihi inda ta zama ta farko, Musulma kuma me sanye da hijabi da ta kafa wannan Tarihi. Ta kammala karatu daga jami'ar Dearborn Heights inda ta karanci Lauya. Saidai hakan ya tayarwa Amurkawa fararen fata hankali sosai inda suke tambayar ya akai aka bari haka ya faru?
Shugaba Tinubu ya bar Abuja dan ziyara zuwa kasashen Japan da Brazil

Shugaba Tinubu ya bar Abuja dan ziyara zuwa kasashen Japan da Brazil

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bar Abuja a yau, Juma'a dan zuwa kasashen Japan da Brazil ziyara. Shugaban zai tsaya a Dubai, UAE kamin ya ci gaba da tafiyar tasa. Shugaba Tinubu ya tashi daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 11:15 na safiyar yau. Manyan jami'an gwamnati da suka hada da shugaban ma'aikatan fadar Gwamnati, Femi Gbajabiamila, da babban me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Ministan kudi, Wale Edun sun halarci filin jirgin.
Kungiyar malaman kwalejojin Kimiyya da fasaha, ASUP sun baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin akwanaki 21 a biya musu bukatunsu ko su tafi yajin aiki

Kungiyar malaman kwalejojin Kimiyya da fasaha, ASUP sun baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin akwanaki 21 a biya musu bukatunsu ko su tafi yajin aiki

Duk Labarai
Kungiyar malaman Kwalejojin Ilimin Kimiyya da Fasaha ASUP ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 21 a biya musu bukatunsu ko su tafi yajin aiki. Shugaban kungiyar, Comrade Shammah Kpanja ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma'a. Yace daya daga cikin abubuwan da suke bukata shine a kafa hukuma me kula da ayyukan kwalejojin Ilimin kimiyya da fasaha. Sannan kuma ya kara da cewa auna neman a daidaita sakamakon kammaga kwalejojin ilimin kimiyya na HND da Kwalin Digiri da ake bayarwa bayan kammala Jami'o'i.