Thursday, November 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Farashin dala a kasuwar Chanji a yau, Litinin

Farashin dala a kasuwar Chanji a yau, Litinin

Duk Labarai
Farashin dala a kasuwar canji ta Gwamnati a yau, Litinin, 30 ga watan Maris ana sayen dalar akan Naira ₦1,382.18 ne. A ranar Juma'a data gabata, an kulle kasuwar da farashin Naira ₦1,384.25 wanda hakan ke nuna darajar Naira ta dan farfado da kaso 0.15 cikin 100. A kasuwar bayab fage kuwa dake Legas, Abuja da Kano, farashin dalar ya kai Naira ₦1,405 zuwa Naira ₦1,420 akan kowace dala.
Kalli Bidiyon yanda HISBAH ta kama wani mutum a gidan Qaruwa yana tsaka da abinda bai dace ba

Kalli Bidiyon yanda HISBAH ta kama wani mutum a gidan Qaruwa yana tsaka da abinda bai dace ba

Duk Labarai
Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta kai samame gidan Qaruwai inda ta kama yawanci 'yan kudu ta mayar dasu garuruwansu. A yayin samamen an kama wani mutum yayin da ya shiga dakin wata Qaruwa. A Bidiyon da ya watsu a kafafen sadarwa an ganshi ana ta kokawa dashi a kokarin fitar dashi daga dakin. https://www.tiktok.com/@y.m.y.ingawa/video/7622732849308781845?_r=1&_t=ZS-9571OKVL3Rp&sp_source=7537614245375297080
Kalli Bidiyon: Abinda Peter Obi yayi bayan da aka fara sallar Gawar Mahaifiyar Malam Nasiru Ahmad El-Rufai shi kuma yana cikin masallacin

Kalli Bidiyon: Abinda Peter Obi yayi bayan da aka fara sallar Gawar Mahaifiyar Malam Nasiru Ahmad El-Rufai shi kuma yana cikin masallacin

Duk Labarai
Peter Obi yana cikin babban masallacin Juma'a na Abuja yayin da aka kabbara sallar gawar mahaifiyar malam Nasiru Ahmad El-Rufai. An hango Peter Obi tsaye a cikin masallacin inda ya kalli kudu yayin da Musulmai suka kalli gabas suna sallar Lamarin ya dauki hankula a kafafen sadarwa. https://twitter.com/i/status/2038293691316507019
Allah Sarki kalli Bidiyon yanda Farfesa Isa Ali Pantami ya shirya Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani da tsohon Gwamnan Jihar  Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a wajan jana’izar mahaifiyarsa

Allah Sarki kalli Bidiyon yanda Farfesa Isa Ali Pantami ya shirya Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani da tsohon Gwamnan Jihar Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a wajan jana’izar mahaifiyarsa

Duk Labarai
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya shirya gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani da tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai. Yayi wannan shiri ne a wajan jana'izar mahaifiyar El-Rufai da aa yi a Kano. An ga yanda yasa suka gaisa uwa yace su yafewa juna. https://twitter.com/i/status/2038282643507183811 https://www.tiktok.com/@hon.gkata/video/7622761880288791829?_r=1&_t=ZS-956RDpVMplp&sp_source=7537614245375297080
Na sadaukar da Albashina gaba daya tun daga farkon hawan mulkina a baiwa Iyalan sojojin da suka rigamu gidan gaskiya da kuma wanda suka jikata>>Inji Shugaba Tinubu

Na sadaukar da Albashina gaba daya tun daga farkon hawan mulkina a baiwa Iyalan sojojin da suka rigamu gidan gaskiya da kuma wanda suka jikata>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya sadaukar da Albashinsa gaba daya tun daga hawansa mulki a 2023 zuwa ga iyalan sojoji da suka rigamu gidan gaskiya da kuma wadanda suka jikkata. Shugaba Tinubu yace an bude wani asusu ne na musamman dan tallafawa irin wadannan sojoji da iyalansu, kuma shine shi ya fara saka tasa Gudummawar. Yace yana kira ga Gwamnoni, Sanatoci da sauran 'yan kasuwa da abokan sa suma su saka nasu gudummawar. Ya bayyana cewa aikin na sojoji sadaukarwa ce wadda bai kamata a barta haka ba.
Dole kowa ya gayawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu kuma ya biya haraji nan da 31 Maris

Dole kowa ya gayawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu kuma ya biya haraji nan da 31 Maris

Duk Labarai
Tarar Naira dubu Dari(100,000) ce duk wanda bai gayawa Gwamnati yawan kudin da yake samu ba sannan ya biya haraji nan da ranar 31 ga watan Maris zai biya. Dokar tace kamin nan da ranar 31 ga watan Maris dolene kowane dan Najeriya ya gayawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu sannan ya biya Haraji. Hakanan dokar tace duk wanda bai yi hakan ba za'a ci shi tarar Naira dubu dari(100,000) sannan za'a ci gaba da cinsa tarar Naira dubu hamsin(50,000) kowane wata da yaki fadawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu kuma yaki biyan Haraji Yanda mutum zai gayawa Gwamnati yawan kudaden da yake samu shine: Ka samu Lambar biyan Haraji da ake cewa TIN. Ka Shiga E tax portal na jiharka. Saika cie duka bayanan da ake da bukata.
Kalli Bidiyon yanda aka bugawa mutanen da suka je babban taron jam’iyyar APC a Abuja Hayaki me sa hawaye

Kalli Bidiyon yanda aka bugawa mutanen da suka je babban taron jam’iyyar APC a Abuja Hayaki me sa hawaye

Duk Labarai
Wannan Bidiyon ya dauki hankula sosai a kafafen sada zumunta bayan da aka ga wanda suka je taron jam'iyyar APC na kasa a Abuja an buga musu barkonon Tsohuwa. Da yawa dai sun rika musu Allah ya kara. https://www.tiktok.com/@italoo.jesus.1111/video/7622266775413083399?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7622266775413083399&source=h5_m&timestamp=1774707469&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7606977366144993025&share_link_id=f9b38912-d2ce-4aea-a5b2-69b91dd57ffc&share_app_id=123...