Kashi 60 na abinci a Najeriya na lalacewa saboda rashin wuraren adana – NAFDAC
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC), ta ce kashi 60 na abinci a Najeriya na lalacewa ne sakamakon rashin wuraren adana abinci da suka dace.
Darakta-janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana haka a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels, inda ta ce wuraren adana abinci sun yi kaɗan a ƙasar.
Ta ce idan aka samu wuraren adana abinci masu kyau, dangin abinci irin ganyayyaki da su tumatiri duka ba za su ci gaba da lalacewa ba.
Ta ce hakan ne ya sa suke ɗuakar matakai na ganin abinci da ake adanawa sun ɗauki lokaci ba su lalace ba ta hanyar samar da wuraren adana na zamani.








