Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

INEC ta saka ranar fara rajistar masu zaɓe a faɗin Najeriya

INEC ta saka ranar fara rajistar masu zaɓe a faɗin Najeriya

Duk Labarai
Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027. Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma'a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki. Hukumar zaɓen ta kuma saka ranar Litinin 25 ga watan Agustan a matsayin ranar fara rajistar a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi da sauran wuraren da ta ware don gudanar da aikin. INEC ta ce za a riƙa gudanar da aikin ne daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Juma'a. Kan hakan ne hukumar ta buƙaci waɗanda ba su da rajistar su yi amfani da damar wajen mallakar rajistar. Hukumar ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun yin rajistar zaɓe a Najeriya....
Kalli Bidiyon: Idan da hakkina a Miliyan 152 da aka rabawa kowace cikin ‘yan kwallo mata ‘yan Najeriya ban yafe ba>>Inji Malam

Kalli Bidiyon: Idan da hakkina a Miliyan 152 da aka rabawa kowace cikin ‘yan kwallo mata ‘yan Najeriya ban yafe ba>>Inji Malam

Duk Labarai
Wannan malamin ya bayyana cewa, idan da hakkinsa a cikin Naira Miliyan 152 ds aka baiwa kowanne daga cikin 'yan mata 'yan kwallon kafa na Najeriya, watau Super Falcons da suka ciwo kofin Afrika bai yafe ba. Malam ya bayyana hakane yayin hudubar Juma'a. Ya bayyana takaicin yanda ba'a magance matsalar tsaro ba amma gashi ana rabawa 'yan kwallo kudade. Kudaden da aka rabawa 'yan matan sun jawo cece-kuce sosai. https://www.tiktok.com/@jan_zaki03/video/7533637041154723080?_t=ZS-8yWboFNJitN&_r=1
Allah Sarki: Kalli Bidiyo yanda Adam A. Zango ya dawo ya ci gaba da fim bayan kammala jinya

Allah Sarki: Kalli Bidiyo yanda Adam A. Zango ya dawo ya ci gaba da fim bayan kammala jinya

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya samu sauki sosai bayan hadarin motar da yayi wanda yayi sanadiyyar kwa ciyarsa a asibiti. Adam A. Zango dai an ganshi a location wajan daukar fim. Kamin nan mun kawo muku cewa, jaruman Kannywood sun shiryawa Adam A. Zango liyafa ta musamman dan bikin dawowarsa ci gaba da sana'a. https://www.tiktok.com/@kannywoodtv1/video/7533577488556035351?_t=ZS-8yWZoGpmMjZ&_r=1 Hakanan shima Adam A. Zangon ya wallafa a shafinsa na Tiktok inda yake cewa yana samun sauki sosai. https://www.tiktok.com/@iam_adam_a_zango/video/7533647058620779781?_t=ZS-8yWaH4JcDbd&_r=1 Adam A. Zango ya daga kafarsa inda aka ga har yanzu akwai bandeji akai.

Ku Yi Amfani da Shafukan Sada Zumunta Wajen Ƙarfafawa Ƙasa, Ba Raba Kan Jama’a Ba, Sakon Shugaba Tinubu Ga Matasa

Duk Labarai
Ku Yi Amfani da Shafukan Sada Zumunta Wajen Ƙarfafawa Ƙasa, Ba Raba Kan Jama’a Ba, Sakon Shugaba Tinubu Ga Matasa. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga matasan Najeriya da ke da tasiri a kafofin sadarwar zamani da su yi amfani da wannan damar wajen haɗa kan al’umma da ƙarfafa cigaban ƙasa. Ya jaddada muhimmancin tantance gaskiyar bayanai kafin yada su, yana mai cewa karfin da kafafen ke da shi na da tasiri a fagen cigaba da haɗin kai haka kuma amfani da su ta mummunar hanya na iya haifar da rikici. Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron Progressives Digital Media Summit da aka gudanar a Abuja, mai taken “Unveiling the Critical Role of New Media in National Development.” Ya ce matasa sun fara nuna kwarewa ta hanyar kirkire-kirkire da amfani da fasahar zamani do...
Shugaba Tinubu ya suke Gawuna daga shugaban Kwamitin gudanarwa na jami’ar Bayero dake Kano

Shugaba Tinubu ya suke Gawuna daga shugaban Kwamitin gudanarwa na jami’ar Bayero dake Kano

Duk Labarai
Shuagaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada AVM Sadiq Ismail Kaita a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwa na jami'ar Bayero dake Kano. Kaita ya maye Dr. Nasiru Yusuf Gawunane a wannan mukami. Gawuna kuma shine shugaban hukumar kula da gidaje ta kasa. A sanarwar da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar Yace an cire gawuna daga shugabancin kwamitin gudanarwa na BUK ne dan ya mayar da hankali kan shugabancin hukumar kula da gidaje ta kasa Gawuna dai na hannun damar tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne.
Kungiyar kare hakkin musulmai ta Najeriya, MURIC ta nemi Gwamnati ta gina kotunan shari’ar Musulunci a kowace jiha

Kungiyar kare hakkin musulmai ta Najeriya, MURIC ta nemi Gwamnati ta gina kotunan shari’ar Musulunci a kowace jiha

Duk Labarai
Kungiyar dake ikirarin kare hakkin Musulmai a Najeriya, MURIC ta bukaci Gwamnatin tarayya ta gina Kotunan shari'ar Musulunci a kowace jiha dake kasarnan. Kungiyar tace dokar da ake amfani da ita babu adalci a ciki kuma akwai wasu sassa na kasarnan da babu kotunan Shari'a shiyasa take gabatar da wannan bukata. Kungiyar tace dan hakane take bukatar gwamnatin tarayya kamar yanda aka gina manyan kotunan gwamnatin tarayya a kowace jiha to itama kotun shari'ar Musulunci a ginata a kowace jihar. Shugaban kungiyar, Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Karya ministan Lafiya yake, bamu janye yajin aiki ba>>Inji Kungiyar malaman Jinya(Nurse) na Najeriya

Karya ministan Lafiya yake, bamu janye yajin aiki ba>>Inji Kungiyar malaman Jinya(Nurse) na Najeriya

Duk Labarai
Kungiyar malaman jinya(Nurse) da Ungozoma (NANNM-FHI) sun bayyana cewa, basu janye yajin aikin da suka shiga ba na kwanaki 7. Kungiyar ta nesanta kanta da kalaman Ministan lafiya, Prof. Muhammad Pate wanda a dazu bayan kammala zaman tattaunawa dasu yace sun amince su janye yajin aikin. Me magana da yawun kungiyar, Omomo Tibiebi ne ya bayyana haka inda yacw yajin aikin da suka fara tun ranar Laraba har yanzu basu janye ba. Yace ba ministan ne ya ke yajin aikin ba, dan haka bashi da hurumin janye yajin aikin. Yace sai a ranar Asabar ne zasu zauna dan tattauna batun da duba irin alkawarin da gwamnatin ta musu ko abune da zasu iya amincewa dashi ko kuwa a'a.
Karanta Jadawalin shekarun Gwamnonin Najeriya, Ko Gwamnan jiharku shekarunsa nawa?

Karanta Jadawalin shekarun Gwamnonin Najeriya, Ko Gwamnan jiharku shekarunsa nawa?

Duk Labarai
Wannan Jadawalin shekarun Gwamnonin Najeriya ne: Bala Muhammed (Bauchi): 66 years Douye Diri (Bayelsa): 66 years Hope Uzodinma (Imo): 66 years Charles Soludo (Anambra): 65 years Bassey Otu (Cross River): 65 years Abdulrahman Abdulrasaq (Kwara): 65 years Abdullahi Sule (Nasarawa): 65 years Dapo Abiodun (Ogun): 65 years Ademola Adeleke (Osun): 65 years Muhammad Yahaya (Gombe): 63 years Sheriff Oborevwori (Delta): 62 years Umar Namadi (Jigawa): 62 years Abba Kabir Yusuf (Kano): 62 years Umo Eno (Akwa Ibom): 61 years Alex Otti (Abia): 60 years Babajide Sanwo-Olu (Lagos): 60 years Lucky Aiyedatiwa (Ondo): 60 years Caleb Mutfwang (Plateau): 60 years Nasir Idris (Kebbi): 59 years Dauda Lawal (Zamfara): 59 years Hyacinth Alia (Ben...