Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: Aliko Dangote ya sauka daga shugabancin kamfaninshi na Simintin Dangote dan mayar da hankali kan Matatar mansa

Da Duminsa: Aliko Dangote ya sauka daga shugabancin kamfaninshi na Simintin Dangote dan mayar da hankali kan Matatar mansa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Dangote ya sauka daga shugabancin kamfanin sa na Siminti inda zai mayar da hankali kan matatar mansa. Me magana da yawun kamfanin nasa na Siminti, Anthony Chiejina ne ya bayyana hakan. Yace an nada Emmanuel Ikazoboh a matsayin sabon shugaban kamfanin simintin na Dangote. Yace hakanan an baiwa Hajiya Mariya Aliko Dangote mukamin daga daga cikin masu gudanarwa na kamfanin.
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda mutane sukai ta kuka bayan kallon hirar da aka yi da  tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Nuhu

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda mutane sukai ta kuka bayan kallon hirar da aka yi da tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Nuhu

Duk Labarai
Bayan bayyanar hirar da Hadiza Gabon ta yi da tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu inda aka ganta tana kuka tana bayar da labarin irin jarabawar data tsinci kanta a ciki, mutane da yawa sun tausaya mata. Da yawa musamman mata, sun koka da hawaye bisa irin halin da suka ga tsohuwar jarumar a ciki. Da yawa sun dora Bidiyon su suna kuka wasu kuma na kiran a tallafawa Ummi Nuhu: https://www.tiktok.com/@iya_habu/video/7530991161511562501?_t=ZM-8yKQVh3VkmL&_r=1 https://www.tiktok.com/@officielhassanmakeup227/video/7530979471470365958?_t=ZM-8yKQam1m6tC&_r=1 https://www.tiktok.com/@hawee_maiduguri/video/7530943228003044609?_t=ZM-8yKQeS1dwW5&_r=1
Kalli Bidiyon: Iyayen wannan yarinyar na ta shan yabo saboda ta ki amincewa dan ajinsu ya mata rubutu a jikin kayanta irin wanda ake yi bayan an kammala makaranta

Kalli Bidiyon: Iyayen wannan yarinyar na ta shan yabo saboda ta ki amincewa dan ajinsu ya mata rubutu a jikin kayanta irin wanda ake yi bayan an kammala makaranta

Duk Labarai
Wannan wata matashiyace da iyayenta ke ta shan yabo sosai a kafafen sada zumunta bayan abinda da aikata. Yarinyar dai taki amincewa ne abokin karatunta ya mata rubutu a jikin kayan ta irin wanda ake yi dinnan bayan an kammala karatu. Da ya takura sai ya mata a karshw ta falla masa mari. https://www.tiktok.com/@binsadeeq02/video/7530645650904468758?_t=ZM-8yKOHOAdN4y&_r=1 Da yawa sun jinjina mata sosai, har wani ya mata kyautar kudi.
Kalli Bidiyon: Aske Gashin Hammata ya fi Maulidi Daraja>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Kalli Bidiyon: Aske Gashin Hammata ya fi Maulidi Daraja>>Inji Malam Ibrahim Matayassara

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Ibrahim Matayassara ya bayyana cewa, Aske gashin hammata yafi Maulidi Daraja. Malamin ya bayyana hakane a wani Bidiyo sa da ya watsu sosai a kafafen sadarwa. Yace dalili kuwa shine ga babin Aske gashin hammata yazo a karatu amma babin Maulidi be zo ba. https://www.tiktok.com/@ibrahimmatayassara/video/7530911491805990149?_t=ZM-8yKN1MpBHza&_r=1
Ƴansandan sun kama mutumin da ake zargi da kashe tsohuwar matarsa

Ƴansandan sun kama mutumin da ake zargi da kashe tsohuwar matarsa

Duk Labarai
Ƴansandan Najeriya reshen Jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum mai suna Iliyasu Musa, ɗan shekara 40, bisa zargin kashe tsohuwar matarsa Hadiza Sale, ƴar shekara 30, a ƙauyen Afasha da ke ƙaramar hukumar Aujara. Wanda ake zargin ya shafe sama da makonni biyu yana ɓuya tun bayan da lamarin ya faru a ranar 10 ga Yuli, 2025. Ana zargin mutumin da kashe matar ne ta yin amfani da sanda sa'ilin da take kan hanyar komawa gida bayan ta dawo daga kasuwa da daddare. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, kakakinta SP Shi'isu Lawan Adam ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga ofishin Aujara ne suka samu nasarar kama shi a ranar Talata, 23 ga Yuli, 2025 a ƙauyen Larabar-Tambarin-Gwani bayan tsantsan bibiyarsa da suka yi da kuma tura jami’ai na musamman don gano inda yake ɓuya., Rundu...
Najeriya na shirin kwaso ‘yan ƙasarta da suka maƙale a Afirka ta Tsakiya

Najeriya na shirin kwaso ‘yan ƙasarta da suka maƙale a Afirka ta Tsakiya

Duk Labarai
Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara ƙoƙarin mayar da wasu ‘yan kasar da suka maƙale kuma suke gararamba a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zuwa gida. Wannan na zuwa ne bayan wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka yi watsi da mutanen cikin mawuyacin hali a yankin Bambari mai nisan kilomita 850 daga Bangui babban birnin kasar. Wata sanarwa da Ma'iaktar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta ce tuni ofishin jakadancin ƙasar a Bangui ya tuntuɓi mutanen. "An karɓo fasfunansu kuma an tura motar da za ta ɗauko su daga Bambara zuwa Bangui," a cewar sanarwar. "Ana sa ran za su isa Bangui bisa rakiyar jami'an tsaro a ranar Asabar."