Dama ita harkar fim haka take, ba’a gamata Lafiya>>Inji Aminu J. Town
Mawaki, Aminu J. Town ya bayyana cewa, Haka harkar fim take ba'a gama ta lafiya.
Ya bayyana hakane a wani podcast da aka yi dashi inda yace ko dai mutum yayi mutuwar wulakanci ko kuma a zo ana nema mai taimako haka 'yan fim ke karewa.
Hakan na zuwane bayan dambarwar tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu wadda ta bayyana a shirin Gabon Show abin tausai
Tuni dai har an fara taimakawa Ummi Nuhu ganin halin data tsinci kanta.
https://www.tiktok.com/@y_america1/video/7531529657653497094?_t=ZM-8yO1kBcgCTW&_r=1








