Saturday, December 21
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Kalli Bidiyon Rahama Sadau da ya jawo cece-kuce, wasu na tambayar ‘Ke Musulmace?’

Kalli Bidiyon Rahama Sadau da ya jawo cece-kuce, wasu na tambayar ‘Ke Musulmace?’

Rahama Sadau
Tauraruwar Fina-finan Hausa, India da kudancin Najeriya, Rahama Sadau ta dauki hankula bayan wallafa wani bidiyo da ya dauki hankula a kafafen sada zumunta. Rahama ta yi shiga da wata bakar doguwar riga da ta matseta kuma ta nuna wasu sassa na jikinta. A Bidiyon an ga Rahama tana juyi da rungumar abokan huldarta maza da mata. Kalli Bidiyon anan Wasu da suka bayyana ra'ayoyinsu akan Bidiyon sun rika bayyana mamaki inda wata me suka Azeemah Giwa ta tambayi shin Rahamar Musulmace? Wani kuma me suna Kabeer cewa Rahamar Yayi ama baki tunanin sakamakon abinda kike yi. Wani kuwa cewa yayi,fim din Hausa ne Sanadi. Saidai wasu kuma da dama sun yabeta
Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1, karanta yanda zaku nema

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1, karanta yanda zaku nema

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, ta fara turawa mutane bashin Naira Miliyan 1 da aka nema a baya. Bashin dai ana bayar dashi ne ga mutane wanda kamfanoninsu ko kasuwancinsu ke da rijistar CAC. Gwamnatin tarayya ta ware Naira Biliyan 75 dan baiwa mamfanoni ko kasuwanci masu rijista bashin Naira Miliyan 1 kowannensu. Bashin dai baya bukatar ka bayar da jingina saidai akwai kudin ruwa na kaso 9 cikin 100. Ana bayar da bashinne ta hanyar bankin Bank of Industry. Babban me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar samar da ayyuka da kananan masana'antu Temitola Adekunle-Johnson ne ya bayyana haka a yau Laraba. Tuni dai aka fara wannan shiri a jihohin Ogun, Bauchi, Enugu, Kaduna.
Ya kamata Gwamnonin Arewa su canja matsaya akan kin amincewa da kudirin dokar Haraji da Shugaba Tinubu ya kawo,abu ne me kyau da zai karawa gwamnati hanyar kudaden shiga>>Inji Sanata Shehu Sani

Ya kamata Gwamnonin Arewa su canja matsaya akan kin amincewa da kudirin dokar Haraji da Shugaba Tinubu ya kawo,abu ne me kyau da zai karawa gwamnati hanyar kudaden shiga>>Inji Sanata Shehu Sani

Duk Labarai
Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana cewa, yana jawo hankalin Gwamnonin Arewa da su canja matsaya akan kin amincewa da kudirin gyaran haraji da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ke son yi. Yace kudirin abu ne me kyau da zai karawa gwamnati hanyoyin kudaden shiga. Sannan yace yana baiwa Gwamnonin shawarar su karanta kudirin dokar dan su fahimceshi. Sanata Shehu Sani dai ya bayyana cewa, babu inda aka ce za'a kara yawan harajin da ake karba a kudurin kuma babu inda aka ce kudirin zai sa a samu raguwar ayyukan yi ko kuma cutar wani yanki na kasarnan. The Tax reform Bill is not inimical to the North or any part of this country.Its in fact economically beneficial and fair to all parts.People should keep aside sentiments and read the Bill carefully.Its a comprehensive and...
Dogarin Sanata Barau Jibrin ya rasu

Dogarin Sanata Barau Jibrin ya rasu

Duk Labarai
Sanata Barau I. Jibrin yayi alhinin rasuwar daya daga cikin hadimansa me suna Corporal Barde Nuhu da ya rasu a hadarin mota. Corporal Barde Nuhu ya rasune a yayin da yake kan hanyar zuwa gida jihar Naija dan ganawa da iyalansa. Yana kan hanyar zuwa Kauyen Shata ne dake karamar hukumar Bosso a jihar ta Naija yayin da hadarin ya rutsa dashi. Sanata Barau a sanarwar da ya fitar ta bakin kakakinsa, Ismail Mudashir yace Barde hazikine sosai wajan aiki. Yace yana mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin da kuma hukumar 'yansandan Najeriya.
Hoto: Davido ya nuna yanda yayi zabe a kasar Amurka, Saidai ‘yan kasar Africa ta kudu sunce karya yake a bola ya dauki kuri’ar yayi hoto da ita dan ace shi dan America ne

Hoto: Davido ya nuna yanda yayi zabe a kasar Amurka, Saidai ‘yan kasar Africa ta kudu sunce karya yake a bola ya dauki kuri’ar yayi hoto da ita dan ace shi dan America ne

Duk Labarai
Shahararren mawakin Najeriya, Davido ya nuna kuri'arsa bayan yayi zabe a kasar Amurka. Saidai lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta. Yayin da 'yan Najeriya ke yaba masa, 'Yan kasar Africa ta kudu kuwa zolayarsa suke inda wani yace karya yake a bola ya dauki kuri'ar ya dauki hoto da ita kawai dan yayi karya.
Najeriya ta kashe Naira Tiriliyan 4.4 wajan biyan bashi

Najeriya ta kashe Naira Tiriliyan 4.4 wajan biyan bashi

Duk Labarai
Babban bankin Najeriya ya nuna cewa,Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Triliyan 4.4 wajan biyan bashi a watanni 3 na biyu na wannan shekarar watau tsakanin watannin April, May da June. Jimullar kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe a cikin wadannan watanni 3 Naira Tiriliyan 6.8 ne gaba daya wanda daga ciki ne aka cire Naira Tiriliyan 4.4 aka biyawa Najeriyar bashi watau dai Naira 2.4 ne suka yi saurawa gwamnati ta gudanar da sauran ayyukan kasa dasu. Hakan na nufin kaso 64.7 cikin 100 ne gwamnatin ta kashe wajan biyan bashi daga cikin kudaden shigarta. Hakan kuma na nufin Najeriya ta kashe fiye da abinda take samu a tsakanin wadannan watannin. Jimullar bashin da ake bin Najeriya dai ya kai Naira 121.67.
Atiku Abubakar ya taya Donald Trump murnar lashe zaben shugaban kasar Amurka

Atiku Abubakar ya taya Donald Trump murnar lashe zaben shugaban kasar Amurka

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya taya shugaban kasar Amurka, Donald Trump murnar lashe zaben shugaban kasar. A sakon da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Atiku ya bayyana Tsarin Dimokradiyya a matsayin mafi dacewa duk da yana da matsalolinsa. Atiku ya kuma bayyana cewa irin gwagwarmayar da Donald Trump ya sha kamin ya zama shugaban kasar darasine babba da ya kamata a lura dashi. Hakanan Atiku ya kuma taya Donald Trump da mutanen kasar Amurka murnar nasarar zaben inda yace yana fatan Donald Trump din zai taimaka wajan aiwatar da zaben gaskiya a Najeriya da sauran kasashen Duniya.
Tinubu ya taya Donald Trump murna

Tinubu ya taya Donald Trump murna

Duk Labarai
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taya Donald Trump murna, inda ya ce a shirye yake su ci gaba da aiki tare domin inganta alaƙa tsakanin Najeriya da Amurka. Ya ce, "idan muka haɗa kai, za mu inganta tattalin arziki da zaman lafiya da magance matsalolin da al'umarmu ke fuskanta," kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya sanar. Trump ne dai ya sanar da samun nasararsa a jawabinsa ga magoya bayansa, inda ya ce ya samu gagarumar nasara. Tinubu ya kuma yaba wa Amurkawa bisa yadda suka gudanar da zaɓen cikin lumana. Tinubu ya ce kasancewar Trump ya taɓa yin mulkin ƙasar, dawowarsa a matsayin shugaban ƙasar na 47 zai zo da gagarumar sauyi a tattalin arziki da ƙarin haɗin kai tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.