Saturday, April 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Dalilin da yasa duk da zuwan sojojin Amurka Najeriya ba’a fara ganin habakar tsaro ba>>Injin Hukumar sojoji Najeriya

Dalilin da yasa duk da zuwan sojojin Amurka Najeriya ba’a fara ganin habakar tsaro ba>>Injin Hukumar sojoji Najeriya

Duk Labarai
Hukumar sojojin Najeriya ta baiwa 'yan Najeriya hakuri saboda rashin ganin canji a harkar tsaro duk da zuwan sojojin Amirka. Me magana yawun hukumar Major General Micheal Onoja ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai. Yace sojojin na Amirka suna aikin bayar da bayanan sirri ne amma basa yaki. Yace 'yan Najeriya su yi hakuri sai a hankali za'a fara ganin Chanji.
Da Duminsa: Na fasa ziyarar da na yi niyyar kaiwa jihar Ogun, saboda abinda ya faru a jihar Filato>>Inji Shugaba Tinubu

Da Duminsa: Na fasa ziyarar da na yi niyyar kaiwa jihar Ogun, saboda abinda ya faru a jihar Filato>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya fasa kai ziyarar da yayi niyyar yi zuwa jihar Ogun saboda abinda ya faru a jihar Filato. Yace a yanzu zai kai ziyara jihar Filato ne dan jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa dasu sannan ya basu tabbacin samar da tsaro. Yace daga can zai wuce Legas dan yin hutun good Friday sannan kuma zai yi ziyarar aiki a Lagos din da Ogun da Bayelsa.
Jam’iyyar ADC ka iya samun Tangarda: Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta cire Shugaban ADC na rikon kwarya da sakataren jam’iyyar na Rikon Kwarya daga shafinta

Jam’iyyar ADC ka iya samun Tangarda: Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta cire Shugaban ADC na rikon kwarya da sakataren jam’iyyar na Rikon Kwarya daga shafinta

Duk Labarai
Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta sanar da cire shugaban jam'iyyar ADC na rikon kwarya, David Umahi da sakataren jam'iyyar na rikon kwarya, Rauf Aregbesola daga shafinta na tattara bayanan shuwagabannin jam'iyyun Najeriya. INEC tace ta yi hakanne saboda karar da aka shigar a kotun daukaka kara daga wani bangare na jam'iyyar da basu yadda da shugabancin su David Mark ba. Kwamishinan yada labarai na INEC, Mohammed Kudu Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yace zasu dakata har sai sun ji hukuncin da kotun daukaka karar zata yanke. Wanda ya shigar da karar shine Nafiu Bala Gombe wanda ke ikirarin cewa shine shugaban jam'iyyar ta ADC.
Hukumomi sun kori baturen kasar Amurka da ya shigo Najeriya yake tunzura Kiristoci akan Musulmai

Hukumomi sun kori baturen kasar Amurka da ya shigo Najeriya yake tunzura Kiristoci akan Musulmai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumomin Najeriya sun kori dan kasar Amirkar nan me suna Mr. Alex Barbir wanda ya shigo Najeriya yake tunxura Kiristoci akan Musulmai. Malam Bashir Ahmad wanda tsohon Hadimin shugaban kasa ne ya bayyana hakan ta shafisa na X inda yace wata majiya me karfi ta sanar dashi hakan. https://twitter.com/i/status/2039371038832603359 A baya dai, an yi kiran Hukumomin su dauki mataki akan wannan bature da ba'a amince da salon da ya shigo dashi Najeriya ba.
Mutanen da kuka gani a wajan komawar Kwankwaso ADC kudi aka basu ba soyayyar gaskiyace ba>>Inji Gwamnatin Abba

Mutanen da kuka gani a wajan komawar Kwankwaso ADC kudi aka basu ba soyayyar gaskiyace ba>>Inji Gwamnatin Abba

Duk Labarai
Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa dubban mutanen da suka taru a wajan komawar Rabiu Musa Kwankwaso Jam'iyyar ADC kudi aka basu. Kwamishinan yada labarai na Kano, Ibrahim Waiya ne ya bayyana haka a ganawarsa da AIT. Yace sun san yanda ake yi, idan za'a yi taro ana bi kauyuka akwai wadanda ake baiwa kudi su rika tara maka mutane. Yace a yanzu Abba ya shiga siyasar kasa inda yake damawa da sauran takwarorinsa.
Daga yau Karku kara jiran Umarni, duk inda kuka ga Tshàgyèràn Dhàjì ku Shèkyèshi kawai>>Ministan Tsaro, Christopher Musa ya baiwa sojoji Umarni

Daga yau Karku kara jiran Umarni, duk inda kuka ga Tshàgyèràn Dhàjì ku Shèkyèshi kawai>>Ministan Tsaro, Christopher Musa ya baiwa sojoji Umarni

Duk Labarai
Ministan tsaro, Christopher Musa ya baiwa sojojin Najeriya umarnin kada su sake sauraren umarni, duk inda suka ga dan Bìndìgà su aikashi kiyama. Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai rundunar operations hadin kai dake Maiduguri. Ko sa a baya lokacin yana shugaban sojojin Najeriya, Christopher Musa ya taba bayar da irin wannan umarni wanda ya jawo masa yabo sosai.
Rahoton sun bayyana cewa shugaba Tinubu na shirin sauke Malam Nuhu Ribadu daga Mukamin me bashi shawara kan harkar tsaro

Rahoton sun bayyana cewa shugaba Tinubu na shirin sauke Malam Nuhu Ribadu daga Mukamin me bashi shawara kan harkar tsaro

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin sauke Malam Nuhu Ribadu daga mukamin me bashi shawara akan harkar tsaro. Rahoton yace Malam Nuhu Ribadu na da shirin tsayawa takarar gwamna a jihar Adamawa, wanda na daya daga cikin dalilan saukar tasa. .Inda kuma a wani bangaren rahoton yace shugaba Tinubu na shirin yiwa harkar tsaro garambawul ne. Rahoton dai nata yawo ne a kafafen sada zumunta inda zuwa yanzu fadar shugaban kasa batace uffan akai ba.
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Bidiyoyin sabuwar Tqrzhomqr data barke a Garin Jos Jihar Filato sun dauki hankulan mutane sosai

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un: Bidiyoyin sabuwar Tqrzhomqr data barke a Garin Jos Jihar Filato sun dauki hankulan mutane sosai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa sabuwar Tqrzomq ta barke a birnin Jos na jihar Filato bayan da aka saukaka dokar hana zirga-zirga. An ga Bidiyon kala-kala na yawo a kafafen sada zumunta inda mutane ke guje-guje. A yayin da a wasu yankunan kuma aka ga jami'an tsaro na sintiri. https://twitter.com/i/status/2039324589503741999 https://twitter.com/i/status/2039329059688128946 https://twitter.com/i/status/2039286176381640875